Revelation of John 13

1Macijin kuwa
Waɗansu rubuce rubucen hannu na baya bayan nan suna da Na kuma ne a nan
ya tsaya a bakin teku.

Dabba daga Teku

Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo.
2Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma. 3Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar. 4Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?”

5Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girmankai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arbaʼin da biyu. 6Ta buɗe bakinta don ta yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama. 7Aka ba ta iko ta yaƙi tsarkaka ta kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jamaʼa, harshe da kuma alʼumma. 8Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada-dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.
Ko kuwa rubutacce daga halittar duniya a littafin rai na Ɗan Ragon da aka yanka


9Duk mai kunne ji, bari yǎ ji.

10Duk wanda aka ƙaddara ga bauta,
ga bauta zai tafi.
Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi,
da takobin za a kashe shi.
Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka.

Dabba daga Ƙasa

11Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. 12Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. 13Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu ban mamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. 14Saboda alamun nan da aka ba ta iko ta yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. 15Aka ba ta iko ta ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don ta yi magana ta kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada. 16Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ʼyantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, 17don kada kowa yǎ saya ko yǎ sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta.

18Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yǎ lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.

Copyright information for HauSRK